Abubuwan da Trump zai tattauna da Buhari a Amurka
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nufi Amurka domin ganawa da shugaba Donald Trump wanda ya gayyace shi zuwa fadar White House.
Shugaba Buhari zai bar Najeriya zuwa Amurka a ranar Asabar.
Wata sanarwa da mai ba shugaban na Najeriya shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya fitar ta ce Buhari da Trump za su gana da juna a ranar Litinin tare da cin liyafar abinci a Fadar White House.
Ya ce shugabannin biyu za su tattauna kan batutuwan da suka shafi bunkasa tattalin arziki da yaki da ta'addanci da kuma ci gaban mulkin dimokradiyya a yammacin Afirka.
Shugaba Donald Trump ne dai ya gayyaci Buhari zuwa Amurka a farkon watan Afrilu.
- 'An yi wa kalaman Shugaba Buhari kan matasa mummunar fahimta'
- Buhari ba ya jin shawara - Atiku Abubakar
Wannan ne karon farko da Shugaba Buhari zai gana da Donald Trump a fadarsa ta White House a Washington.
Sanarwar ta kuma ce, shugaba Buhari zai gana da wasu rukunin kamfanonin Amurka a bangaren aikin noma da kiwo da sufurin jiragen sama.
Shugaba Trump ya taba bayyana kasashen Afirka a matsayin "wulakantattu" a cikin watan Janairun da ya gabata, kafin daga bisani shugaban ya musanta.
Ana ganin a yanzu Mista Trump na kokarin inganta huldar Amurka ne da Najeriya, musamman ganin yadda China ke ci gaba da mamaya a Afrika.
A 2017, gwamnatin Trump ta amince ta sayar wa da Najeriya jiragen yaki goma sha biyu da wasu kayayyakin kula da sha'anin tsaro da darajarsu ta kai dala miliyan 600.
A baya, tsohuwar gwamnatin Obama ta ki amincewa da cinikin jiragen, saboda fargaba a kan wasu dalilai.
Wannan ne karo na biyu da shugabannin Amurka suke gayyatar shugaba Buhari Fadar White House.
A shekarar 2015, tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya taba gayyatar shugaban na Najeriya zuwa Washington.
Comments
Post a Comment