Abubuwan da Trump zai tattauna da Buhari a Amurka
Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES Image caption A farkon watan Afrilu Trump ya gayyaci Buhari zuwa White House Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nufi Amurka domin ganawa da shugaba Donald Trump wanda ya gayyace shi zuwa fadar White House. Shugaba Buhari zai bar Najeriya zuwa Amurka a ranar Asabar. Wata sanarwa da mai ba shugaban na Najeriya shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya fitar ta ce Buhari da Trump za su gana da juna a ranar Litinin tare da cin liyafar abinci a Fadar White House. Ya ce shugabannin biyu za su tattauna kan batutuwan da suka shafi bunkasa tattalin arziki da yaki da ta'addanci da kuma ci gaban mulkin dimokradiyya a yammacin Afirka. Shugaba Donald Trump ne dai ya gayyaci Buhari zuwa Amurka a farkon watan Afrilu. 'An yi wa kalaman Shugaba Buhari kan matasa mummunar fahimta' Buhari ba ya jin shawara - Atiku Abubakar Wannan ne karon farko da Shugaba Buhari zai gana da Donald Trump a fadarsa ta White House a Washington. ...